Search
Close this search box.

Hizbullah ta fitar da faifan bidiyo a karon farko da ke nuna wasu Manyan kayan yaki da ta mallaka

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna wani katafaren ginin karkashin kasa da kuma wata babbar hanyar

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna wani katafaren ginin karkashin kasa da kuma wata babbar hanyar sadarwa mai cike da kayan yaki da na’urorin harba makamai masu linzami.

Bidiyon mai taken “Dutsenmu, Karfinmu” ya kunshi kayan yaki samfurin  Imad 4, wanda ke nuna karfin makamai masu linzami na kungiyar.

Hotunan sun bayyana mayakan Hizbullah a cikin katafaren gini na karkashin kasa, tare da bayyana alamun da ke nuna cibiyar da aka kira Imad 4, da kuma nuna ayar kur’ani mai cewa: “Ku shirya musu duk abin da za ku iya na daga karfi.”

Bidiyon ya kuma nuna motocin dauke da mayan makamai masu linzami suna tafiya daga cikin ginin zuwa wata kofa, suna shirya su domin harbawa.

A cikin faifan bidiyon an yi amfani da wasu sassa na jawabin da Sayyed Hassan Nasrallah ya yi, inda ya ce a halin yanzu  gwagwarmaya ta yi  karfi fiye da kowane lokaci a yankin gabas ta tsakiya.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments