Hizbullah Ta Bukaci Sojojin Isra’ila Su Gaggauta Ficewa Daga Lebanon

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta bukaci sojojin Isra’ila da su kammala janyewarsu daga kudancin kasar kamar yadda yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin biyu

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta bukaci sojojin Isra’ila da su kammala janyewarsu daga kudancin kasar kamar yadda yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin biyu suka cimma, ta tanada.

A watan Nuwamba ne Isra’ila da kungiyar suka amince da tsagaita bude wuta da Faransa da Amurka suka shiga tsakani, wanda ya kawo karshen fadan da aka kwashe sama da shekara guda ana gwabzawa.

A karkashin yarjejeniyar dai sojojin Isra’ila za su fice daga kasar Lebanon sannan kuma dakarun Hizbullah za su fice daga kudancin kasar ta Lebanon a tsawon kwanaki 60 da zai kare a ranar Litinin.

Kakakin gwamnatin Isra’ila David Mencer ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa, “An yi wani yunkuri mai kyau inda sojojin Lebanon da UNIFIL suka maye gurbin dakarun Hizbullah, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.”

Mencer bai amsa tambayoyi kai tsaye kan ko Isra’ila ta bukaci a tsawaita yarjejeniyar ba ko kuma sojojinta  za su ci gaba da zama a Lebanon bayan wa’adin kwanaki 60 din.

Kungiyar Hezbollah ta ce, dole ne Isra’ila ta fice daga kasar Lebanon gaba daya, yayin da wa’adin kwanaki 60 na yarjejeniyar tsagaita bude wuta ya zo karshe, ta kuma yi gargadin cewa ba za a amince da karya yarjejeniyar ba.

Gwamnatin Lebanon a nata banagre ta shaidawa masu shiga tsakani na Amurka cewa kin janyewa Isra’ila a kan lokaci zai iya dagula aikin jibge sojojin na Lebanon, kuma hakan zai zama cikas ga kokarin diflomasiyya tun bayan zaben Janar Aoun a matsayin shugaban kasa a ranar 9 ga watan Janairu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments