Hezbollah ta kai hari kan kamfanin kera kayan soji na “Yodifat” na Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta Labanon na ci gaba da gudanar da wasu ayyuka na musamman da kuma kai farmaki kan yankunan arewacin Falastinu

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta Labanon na ci gaba da gudanar da wasu ayyuka na musamman da kuma kai farmaki kan yankunan arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye, a daidai lokacin da ta sanar da kaddamar da farmaki kan kamfanin kera makamai da kayan soji na “Yodevat” da ke kudu maso gabashin birnin Akka.

Hezbollah na ci gaba da kai farmakai da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka a kan yankunan arewacin Palastinu da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye, wanda hakan ke haddasa hasarar rayuka kai tsaye a tsakanin yahudawan sahyuniya ‘yan share wuri zauna.

A cikin shirin farmakin mai take “Khyber Operations” da misalin karfe 7:05 na safiyar yau litinin, dakarun Hizbullah suka kai hari kan kamfanin “Yodivat” na masana’antun soji.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa, wadannan hare-hare na zuwa ne domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu masu tsayin daka a yankin Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayarsu, da kuma kare kasar Labanon da al’ummarta, da kuma mayar da martani ga hare-hare da kisan kiyashi da haramtacciyar kasar Isra’ila ke aiwatarwa a yankin.

A Jiya Lahadi, kungiyar Hizbullah ta kaddamar da wani gagarumin hari ta sama da jirage marasa matuka a yankin masana’antar “Bar Lev”, da ke gabashin Acre.

A cewar jaridar Times of Israel, masana’antar da Hezbollah ke kaiwa hari, wata masana’anta ce ta BAZ Aviation Components Company, wacce aka kafa a shekara ta 1977, wadda yanzu Hizbullah ke neman gurgunta ayyukanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments