Kungiyar Hizbullah ta harba manyan makaman roka daga Kudancin Lebanon zuwa yankunan da ke arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye, wanda ke zama daya daga cikin hare-haren rokoki mafi muni da Isra’ila ta gani tun daga lokacin da ta kaddamar da yaki kan Gaza.
An yi ta jin karar harbe-harbe a yankunan arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye, wanda ke da nisan kilomita 40 daga gabashin Falasdinu da aka mamaye zuwa yankunan arewacin Jenin a yammacin gabar kogin Jordan. Wasu daga cikin matsugunan da aka ji karar sautin harbe-harben suna da nisan kusan kilomita 60 daga layin da aka shata bayan janyewar Isra’ila daga Lebanon.
Kungiyar gwagwarmayar – Hezbollah, ta kai hare-hare sau uku a safiyar wannan Lahadi, a kan yankunan Falasdinawa da ke karkashin mamayar Isra’ila, a matsayin martani ga kisan kiyashin da “Isra’ila” ta yi a cikin makon da ya gabata kan fararen hula na Lebanon.
Farmakin farko kungiyar ta kaddamar da shi ne a kan sansanin sojin Isra’ila da ke Ramat David, da wani sansanin sojin sama na Isra’ila, inda kungiyar ta yi amfani rokoki samfurin Fadi 1 da Fadi 2, Har ila yau, ta kaddamar da farmaki na uku a kan wani
rukunin masana’antu na soja na Rafael da karfe 6:30 na safiyar wannan Lahadi, wanda kuma a wurin ne ake samar da kayan lantarki na Isra’ila, wanda yake a arewacin birnin Haifa.
Hizbullah ta tabbatar da cewa, wadannan hare-hare na goyon bayan al’ummar Palastinu masu tsayin daka a zirin Gaza ne, da kuma goyon bayan gwagwarmayarsu, da kuma wani bangare na martanin farko kan kisan gillar da yahudawan suka yi a yankuna daban-daban na kasar Labanon, a ranakun Talata da Laraba, lokacin da suka tarwatsa dubban na’urorin sadarwa Pagers da kuma na’urorin sadarwa, wanda aka fi sani da walkie-talkies ko kuma oba-oba.