Shugaban majalisar gudanarwa na kungiyar Hizbbulah ta kasar Lebanon Sayyid Hashem Safiyyuddeen ya bayyana cewa HKI ba zata cimma ko da guda daga cikin manufofinta a yankin Tufanul Aksa ba.
Kamfanin dillancin labaran Fars Today na kasar Iran ya nakalto Sayyid Safiyuddeen yana fadar haka a yau Laraba a taron ciki kwanaki 40 da shahadar Sayyid Fu’ad Shukur daya daga daga cikin manya manyan kwamandojojin dakarun kungiyar a birnin Beirut babban birnin kasar sanadiyar wani harin da jirgin yakin HKI wanda ake sarrafa shi daga nesa yayi.
Sayyid Safiyud Deen ya bayyana cewa ba abinda sojoji HKI suke yi a Gaza da kudancin labanon in banda kissan mata da yara wadanda basu san hawa ko sauka ba. Ya kuma kammala da cewa kungiyarsa ta hana HKI sakat a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye kamar yadda kungiyar Hamasa da sauran kungiyoyi da kasashe masu tallafa masu suka hanata sakat a kudanci da sauran wurare a cikin kasar.