Hezbollah ta fara harba manyan makamai a kan sansanin sojin Isra’ila domin daukar fansa

Kungiyar Hizbullah ta harba manyan makaman roka daga Kudancin Lebanon zuwa yankunan da ke arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye,  wanda ke zama daya daga

Kungiyar Hizbullah ta harba manyan makaman roka daga Kudancin Lebanon zuwa yankunan da ke arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye,  wanda ke zama daya daga cikin hare-haren rokoki mafi muni da Isra’ila ta gani tun daga lokacin da ta kaddamar da yaki kan Gaza.

An yi ta jin karar harbe-harbe a yankunan arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye, wanda ke da nisan kilomita 40 daga gabashin Falasdinu da aka mamaye zuwa yankunan arewacin Jenin a yammacin gabar kogin Jordan. Wasu daga cikin matsugunan da aka ji karar sautin harbe-harben suna da nisan kusan kilomita 60 daga layin da aka shata bayan janyewar Isra’ila daga Lebanon.

Kungiyar gwagwarmayar – Hezbollah, ta kai hare-hare sau uku a safiyar wannan Lahadi, a kan yankunan Falasdinawa da ke karkashin mamayar Isra’ila, a matsayin martani ga kisan kiyashin da “Isra’ila” ta yi a cikin makon da ya gabata kan fararen hula na Lebanon.

Farmakin farko kungiyar ta kaddamar da shi ne a kan sansanin sojin Isra’ila da ke Ramat David, da wani sansanin sojin sama na Isra’ila, inda kungiyar ta yi amfani rokoki samfurin Fadi 1 da Fadi 2, Har ila yau, ta kaddamar da farmaki na uku a kan wani

rukunin masana’antu na soja na Rafael da karfe 6:30 na safiyar wannan Lahadi, wanda kuma a wurin ne ake samar da kayan lantarki na Isra’ila, wanda yake a arewacin birnin Haifa.

Hizbullah ta tabbatar da cewa, wadannan hare-hare na goyon bayan al’ummar Palastinu masu tsayin daka a zirin Gaza ne, da kuma goyon bayan gwagwarmayarsu, da kuma wani bangare na martanin farko kan kisan gillar da yahudawan suka yi a yankuna daban-daban na kasar Labanon, a ranakun Talata da Laraba, lokacin da suka tarwatsa dubban na’urorin sadarwa Pagers da kuma na’urorin sadarwa, wanda aka fi sani da walkie-talkies ko kuma oba-oba.

Wani abin lura shi ne cewa, an harba manyan makaman roka daga Kudancin Lebanon zuwa yankunan da ke arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye, wanda ke zama daya daga cikin hare-haren rokoki mafi muni da Isra’ila ta gani tun bayan kaddamar da hare-harenta a Gaza.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce kungiyar Hizbullah ta harba makaman roka masu cin dogon zango 15 333mm, wadanda ke dauke da bama-baman da ke da nauyin kilogiram 175 a sansanin jiragen sama na Ramat David a harin na farko.

A cewar wadannan rahoto, wannan shi ne karon farko da kungiyar Hizbullah ta harba wannan makamin roka a yankunan da Isra’ila ta mamaye tun a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa rokoki takwas ne kawai daga cikin 15 sojojin Isra’ila suka iya kakkabowa.

Rahotanni da dama sun tabbatar da cewa, tun daga daren Juma’a ya zuwa wayewar garin Asabar zuwa safiyar Lahadi, dakarun Hizbullah sun yi ruwan daruruwan makamai masu linzami a kan yankuna daban-daban na arewacin falastinu da Isra’ila ta mamaye, inda akasarin hare-haren sun nufi sansanonin soji ne da kuma cibiyoyin leken asiri.

Kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa hare-haren nata sun yi barna mai yawa ga rundunar sojin Isra’ila, da hakan ya hada hallaka wasu sojojin da kuma jikkata wasu, amma kamar kullum Isra’ila tana boye irin asasrorin da ta samu sakamakon hare-haren Hizbullah.

Hare-haren Isra’ila na ranakun Talata, Laraba da kuma Juma’a, sun sanadiyar yin shaar mutane da dama, da suka hada da mata da kananan yara, da kuma wasu daga cikin mayakan kungiyar Hizbullah, da suka hada da manyan kwamandoji guda biyu.

Sai lamarin ya fuskanci kakkausar suka daga ko’ina cikin fadin duniya, da hakan ya hada har da kasashen tarayyar turai, inda babban jami’i mai kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Josep Borrel ya yi tir da Allah wadai da kakkausar murya kan hare-haren na Isra’ila a Lebanon, tare da in kira da a gudanar da binciken gaggawa kan lamarin, tare da hukunta jami’an Isra’ila da suke da hannua  cikin wannan ta’asa, kamar yadda ita ma majalisar dinkin duniya bayan ta yi Allawadai da lamarin, ta kuma bayyana shi da cewa yana da matukar hadari ga makomar zaman lafiyar yankin da ma duniya baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments