Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, y ace yana fatan sabuwar gwamnatin Siriya za ta dauki Isra’ila a matsayin makiyarta.
A wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Asabar Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa: Muna goyon bayan kasar Siriya ne saboda ta kasance tana kiyayya da Isra’ila kuma muna fatan sabuwar gwamnatin za ta dauki Isra’ila a matsayin makiyarta kuma ba za ta daidaita alakar da ke tsakaninsu ba.
Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa: Mun dakile makiya a manufarsu, alhalin nasarar da makiya suka samu ita ce ta kawar da shugabanninmu ta hanyar shahada su. »
A ci gaba da jawabin nasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya ce, yayin da yake ishara da abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya a baya-bayan nan: Muna fatan dukkanin bangarorin da ke Siriya za su shiga a dama dasu wajen kafa gwamnatin hadaka.
“Ko da yake kungiyar Hizbullah ta rasa hanyar taimakon soja ta Syria; amma abin da ke da muhimmanci shi ne tsayin daka bil hakki,” in ji shi.
“Ba ma tunanin abin da ke faruwa a kasar Siriya zai shafi kasar Lebanon, muna fatan kasar Siriya za ta samu kwanciyar hankali bisa burinta na kasa.”