A jiya Asabar ne dai harkar musulunci a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ta yi zaman juyayin tunawa da kisan kiyashin Zaria karo na 9 da aka yi a birnin Abuja.A shekarar 2015 ne dai sojojin gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin hafsan hafsoshin kasar Laftanar Janar Yusuf Tukur Burutai su ka kai wa Husaniyyar Bakiyyatullah hari, hakan nan kuma gidan Sheikh Ibrahim El-zakzaky a unguwar Gyallesu, sai kuma makarantar Fodiyya a cikin zaria. Bugu da kari sojojin sun kai wani harin a makabatar ‘yan’uwa musulmi ta “Darurrahmah.”
A bisa kididdigar Harkar Musulunci, adadin wadanda su ka kwanta dama sanadiyya hare-haren sun kai 1000 daga ciki har da mata masu ciki da kananan yara.
Sojojin sun ce sun kai wannan harin ne saboda an tare wa Laftanar Janar Burutai hanyarsa ta wucewa.
A wurin bikin, Ibrahim Difa na jami’ar gwamnatin jihar Gombe ya bayyana cewa; “Kisan kiyashin Zaria yana cikin irinsa mafi muni da aka yi a tarihin Nigeria, tun lokacin mulkin mallaka da kuma bayansa”
Bugu da kari, jagoran harkar musulunci ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya gabatar da jawabi a wurin, da a ciki ya bayyana cewa sojojin kasar sun aiwatar abinda wasu kasashe su ka shirya ne da su ka hada Isra’ila da Amurka.
A cikin watan Disamba na 2016 kotun tarayya a Abuja ta wanke Shekin Zakzaky daga zargin aikata laifun da aka yi masa sannan ta bayar da umarnin a sake shi da kuma biyansa diyya.
A ranar 29 ga watan Yuli na 2021 ma wata kotun ta yanke hukuncin a saki Sheikh Zakzaky wanda ake tsare da shi tun a 14 ga watan Disamba na 2015.