Isra’ila ta kara tsananta kai Hare-harenta, inda ta kashe fararen hula akalla 31 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, duk da kokarin da kasashen duniya ke yi na ganiun an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Harin na Isra’ila ya kuma raunata mutane 62 a fadin kasar a ranar Litinin, a cewar ma’aikatar lafiya ta kasar.
Sojojin Isra’ila sun kai hari a yankunan Tayr Harfa da Chamaa a safiyar Talata.
Ko a karshen makon jiya, hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama sun kashe fararen hula akalla 29 a tsakiyar birnin Beirut da kuma wasu da dama a garuruwa daban-daban na kasar Lebanon.
Dangane da harin bam da Isra’ila ta kai ta sama, Hezbollah ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kusan 250 zuwa yankunan arewacin Isra’ila a ranar Lahadi.
Kungiyar Hizbullah ta bayyana wannan hari a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.
Adadin wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Lebanon tun daga ranar 8 ga watan Oktoban 2023 ya haura zuwa 3,768, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 15,699, a cewar ma’aikatar kula da lafiyar jama’a ta Lebanon.