Hare-haren sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da janyo shahada da jikkatan Falasdinawa a birnin Gaza
Rahotonni sun bayyana cewa: Falasdinawa da dama sun yi shahada yayin da wani adadi mai yawa suka samu raunuka sakamakon luguden wuta kan mai uwa da wabi da jiragen saman sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza a yammacin jiya Talata.
Jirgin saman sojojin mamayar Isra’ila ya kai hari kan gidan iyalan Al-Khor da ke kusa da masallacin Abdullah Azzam a unguwar Al-Sabra da ke kudancin birnin Gaza, inda harin ya yi sanadiyarra shahadar Falasdinawa biyar tare da raunata wasu masu yawa.
Rahotannin sun kara da cewa: Sojojin mamayar sun kai hari kan wani gida da ke kusa da masallacin Al-Sousi a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Shati da ke yammacin birnin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu Falasdinawa tare da jikkata wasu na daban.