Hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa 70 tare da raunata 100 a rana guda a yankin da aka yi wa kawanya.
A tsakiyar Gaza, Isra’ilawa sun kai hari kan gidaje da dama a sansanin Nuseirat a ranar Alhamis, inda suka kashe fararen hula 30 tare da jikkata wasu fiye da 50.
Wani harin da aka kai a wani gida da ke yammacin sansanin ya kashe wasu da dama.
A arewacin zirin kuma, an kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu da dama a wani hari ta sama da aka kai a wani gida a yankin Jabalia al-Nazla.
Wannan farmakin ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri a ranar Laraba yana kira da “a tsagaita bude wuta ba tare da sharadi ba kuma na dindindin” a Gaza don kawo karshen yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun watan Oktoban 2023.
Tun lokacin, hare-haren wuce gona da iri da sojojin Isra’ila ke ci gaba da yi sun yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 44,840 tare da jikkata wasu 106,356 a fadin zirin Gaza.