Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ta Gaza Kare Kanta Daga Laifin Kisan Kiyashi Da Take Yi Wa Falasdinawa

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta gaza wajen kubutar da kanta a aiwatar da kisan kiyashin garin Al-Mawasi, inda take ci gaba da fuskantar tofin Allah

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta gaza wajen kubutar da kanta a aiwatar da kisan kiyashin garin Al-Mawasi, inda take ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine

Al’ummu daban-daban na duniya suna ta kiraye-kirayen dorawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila alhakin laifukan da ta aikata a Zirin Gaza musamman ci gaba da yin Allah wadai da kisan kiyashin garin Al-Mawasi da yake birnin Khan Yunus, wanda harin ya lakume rayukan daruruwan Falasdinawa tare da raunata wasu daruruwa na daban, yayin da kasashen duniya da dama suka jaddada yin kira da a hanzarta kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza tare da bayar da kariya ga al’ummar Falastinu.

Martanin yin Allah wadai da laifukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata kan fararen hula na Gaza da kuma kiraye-kirayen kasa da kasa na dorawa sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya alhakin kisan kiyashi da kisan kare dangi da suke yi kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba suna kara yin kamari.

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da makamai masu guban gaske da dokokin kasa da kasa suna amfani su kan al’ummar Gaza, inda ta yi Allah wadai da ci gaba da amfani da makaman a yankunan da suke da yawan jama’a a Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments