Hannayen jarin kamfanonin fina-finan Amurka sun fadi sakamakon barazanar Trump na kakaba harajin kwastam

Bayanai daga Amurka na cewa Hannayen jari na kafofin watsa labaru da kamfanonin shirya fina-finai da harkokin nishadi na Amurka sun fadi kasa, bayan da

Bayanai daga Amurka na cewa Hannayen jari na kafofin watsa labaru da kamfanonin shirya fina-finai da harkokin nishadi na Amurka sun fadi kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, yana shirin kakaba harajin kwastam da kashi 100 bisa 100 a kan fina-finan da ake shiryawa a ketare.

Hannayen jarin kamfanonin fina-finai irin su Netflix Inc. da Warner Bros. Discovery Inc. sun fadi da kusan kashi 3 cikin dari, inda na Paramount Global da Walt Disney Co. kuma suka fadi da kusan kashi 2 cikin dari yayin da aka bude kasuwa.

A wani sakon da ya wallafa kan shafinsa na manhajar True Social, shugaban na Amurka ya ce yana umurtar ma’aikatar kasuwanci da wakilinsa na cinikayya da su “yi maza-maza su fara aikin kakaba” harajin a kan fina-finan kasashen waje, inda ya kara da cewa, “Muna son kara ganin fina-finan da ake yi a Amurka”.

Shugaban ya kuma sanya fina-finan kasashen waje a cikin jerin abubuwan dake kawo barazana ga tsaron kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments