Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki.
“Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin shigar da shi ba a lokacin da jama’a a gefen iyakar ke fama da yunwa, a yayin da muke jin ministocin Isra’ila suna cewa sun ayin hakan ne don matsa lamba kan al’ummar Gaza,” in ji Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher a wata hira a ranar Jumma’a.
Irin wannan na a matsayin laifin yaki ne,” in ji shi.
Baya ga hakan ma a cikin ‘yan kwanakin nan, sojojin Isra’ila sun kashe masu neman agaji da dama a lokacin da suke kokarin isa wurin rarraba kayan agaji a yammacin Rafah a karkashin tsarin Amurka da Isra’ila.
Tuni dai hukumomin agaji na kasa da kasa suka yi gargadin cewa shirin da Isra’ila ke yi na sarrafa rabon kayan agaji a zirin Gaza, ciki har da shawarar da Amurka ke marawa baya, zai kara wahalhalu a yankin Falasdinawa.
A baya-bayan nan ne dai shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi Allah-wadai da sabon salon agajin da Amurka ke marawa baya a Gaza, yana mai cewa “wani cin zarafi” da ke faruwa a can.