Hamas : Ziyarar Ben-Gvir a masallacin al-Aqsa kan iya tayar da yakin addini

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da kutsawa cikin masallacin al-Aqsa da ministan Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya yi a baya bayan nan,

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da kutsawa cikin masallacin al-Aqsa da ministan Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya yi a baya bayan nan, tana mai cewa tana da nufin tayar da “yakin addini” a wannan wuri mai tsarki.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce “Kutsen da Itamar Ben-Gvir, ya yi a cikin masallacin Al-Aqsa mai alfarma, da kuma ziyarar tsokanar da ya kai a harabar masallacin… rashin mutunta ra’ayin musulmi da kuma keta alfarma da matsayin masallacin Al-Aqsa a duniyar Musulunci.”

Kungiyar ta jaddada cewa wannan wulakanci da aka yi yana nuna ” girman kai na wannan gwamnati mai tsattsauran ra’ayi da kuma dagewarta na rura wutar yakin addini.”

Hamas ta kuma bukaci dukkanin kasashen Larabawa da na musulmi masu son ‘yanci da su kare  masallacin Al-Aqsa daga fuskantar karuwar kutse.

Ministan na Isra’ila Ben-Gvir tare da wasu gungun ‘yan Isra’ila sun mamaye harabar masallacin Al-Aqsa da ke gabashin Quds da aka mamaye tare da gudanar da ayyukan ibada a harabar masallacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments