Tashar talabijin din ‘almayadin’ mai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta ambato wani kusa a kungiyar Hamas yana cewa, a zango na biyu na musayar fursunoni tsakaninsu da HKI, za a hada da mayakan Hizbullah ta kasar Lebanon.
A zangon farko na musayar fursunonin dai za saki Falasdinawa da suke a gidajen kurkuku HKI tun gabanin farmakin guguwar Aksa, da kuma mata da kananan yara da aka kama a tsawon lokacin yaki.
A lokacin yakin Lebanon, HKI ta nuna wasu fayafayen bidiyo da a ciki ta nuna wadanda tace mayakan kungiyar Hizbullah ne, ta kama. Sai dai babu wani jawabi da ya fito daga Hizbullah da yake tabbatar da hakan ko korewa.
Za a saki yara da mata 30 na Falasdinawa akan kowane fursuna daya da Hamas take rike da su. Sai kuma wasu fursunonin 30 Falasdinawa marasa lafiya akan kowane Fursuna mai shekara 50 ko maras lafiya dake hannun Hamas.