Hamas ta yi Allah wadai da haramcin da Amurka da EU suka yi wa gidan talabijin na Al-Aqsa

Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da matakin hadin gwiwa da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na hana watsa tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Larabci

Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da matakin hadin gwiwa da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na hana watsa tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Larabci ta Falasdinu da ke da alaka da kungiyar gwagwarmayar.

Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na toshe muryar Falasdinawa.

Sanarwar da Hamas ta fitar ta kara da cewa, wannan shawarar toshe ‘yancin watsa labaru ne da kuma hakki na al’ummar Falasdinu na a ji muryarsu a duniya.”

Hamas ta yi kira ga cibiyoyin yada labarai na kasa da kasa da su yi Allah wadai da wannan shawarar, kuma kada su yi shiru dangane da cin zarafin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai.

Bisa shawarar hadin gwiwa da Amurka da EU suka cimma, za a ci tarar duk wani sashe na tauraron dan adam da ke yada shirye shiryen tashar talabijin ta Al-Aqsa bisa zargin da ake mata na “yada ayyukan ta’addanci.”

Ita ma a nata bangaren, kungiyar Jihad Islami ta Falastinu ta yi tir da haramcin da aka yi wa tashar talabijin din ta Al-Aqsa, tana mai cewa wani hari ne da nufin murkushe muryar Falasdinu da kuma hana al’ummar kasar isar da sakonin ukubar da suke fuskanta ga duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments