Hamas Ta Saki ‘Yan Isra’ila Uku Kan Falasdinawa 369 A Musayar Fursunoni Ta Shida

kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani

kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani musayar fursunonin da aka sako Falasdinawa 369 a wata musanya ta baya-bayan nan a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

An saki ‘yan Isra’ilan uku a birnin Khan Yunus da ke kudancin Gaza, inda Isra’ilawan suka yi jawabi ga jama’a kafin mika su ga kungiyar agaji ta Red Cross.

Sakin dai shi ne na shida tun bayan da tsagaitawar ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu bayan fargabar da ake yi a makon da ya gabata cewa yarjejeniyar ta kusa rugujewa bayan da Isra’ila ta ki ba da isassun kayan agaji a Gaza.

Yawancinsu fursunoni falasdinawan da aka saki wadanda aka kama ne a zirin Gaza bayan harin ba zata da kungiyar ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

Yarjejenitar tsagaita bude wuta ta shiga cikin tsaka mai wuya tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya tayar da cece-kuce kan “kwace” Gaza, da tilastawa mutanen Zirin kaura zuwa Jordan da kuma Masar.

A karkashin Yarjejeniyar tsagaita bude wutar ana sa ran sakin ‘yan Isra’ila 33 yayin kan fursuninin falasdinawa 1,900.

Kawo yanzu an saki Isra’ilawa 16, kan fursunoni 765 na Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments