Hamas Ta Mika Fursinonin HKI 6 Sannan Tana Dakon A Shiga Marhala Ta Biyu

Kungiyar Hamas ta saki yahudawa 6 a marhala ta 7 na musayar fursinoni tsakaninta da HKI karo na 6 a yau Asabar. Tashar talabijin ta

Kungiyar Hamas ta saki yahudawa 6 a marhala ta 7 na musayar fursinoni tsakaninta da HKI karo na 6 a yau Asabar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdiawan na fadar cewa, bayan wannan musaya ta 7, suna dakon a fara marhala ta biyu na yarjeniyar da ke tsakaninta da HKI.

Labarin ya kara da cewa a wannan karon dakarun Hamas sun mika fursinonin yahudawan ne a garin Rafah na kan iyaka da kasar Masar. Kuma kamar yadda aka saba hamas ta mika yahudawan ne ga kungiyar red Cross wanda suke mikasu ga HKI.

Hamas ta bada sanarwan cewa firsononi Falasdinawa 50 wadanda aka yankewa hukuncin kisa, sannan 60 wadanda aka yankewa hukuncin mai tsawo, da 50 wadanda ake tsare da sub a tare da bayyana laifinsu ne HKI zata sake su a wannan musayar. Banda haka wasu 445 wadanda HKI take tsare da su a Gaza tun 7 ga watan Octoba ne za’a sallama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments