Hamas ta gabatar da shawara kan yarjejeniyar musayar fursunoni da tsagaita wuta

Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar

Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar musayar fursunoni, da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar Isra’ila daga yankin, da kuma kaddamar da yunkurin sake gina yankin.

A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar, al-Hayya ya bayyana cewa, kungiyar Hamas a shirye take ta sako dukkan fursunonin da ‘yan gwagwarmaya ke tsare da su domin samun adadin fursunonin Falasdinawa da aka amince da su a halin yanzu da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.

Ya jaddada cewa, dole ne irin wannan yarjejeniyar ta hada da dakatar da yakin gaba daya, da janyewar sojojin Isra’ila baki daya daga Gaza, da fara aikin sake gina yankin, da kuma kawo karshen killacewar da ake yi wa yankin.

Al-Hayya ya yi maraba da kalaman na baya-bayan nan da Adam Boehler, wakilin Amurka a karkashin Shugaba Donald Trump ya yi, wanda ya bayar da shawarar magance matsalolin fursunonin da yakin da ake yi.

Al-Hayya ya bayyana matsayar Boehler a matsayin shawara mai kyau kuma ta daidai da mahangar Hama,s sannan ya nanata shirin kungiyar na cimma cikakkiyar yarjejeniya a karkashin wadannan sharudda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments