Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa, akwai alamun Natanyahu Firai ministan HKI yana son ya sake komawa yaki a Gaza.
Hamdan ya ce, kafin haka gwamnatin HKI ta dakatar da aikin aiwatar da yarjeniyar da suka kulla da ita, yana son ya yi watsi da ita, sannan ya bukaci a sake tattaunawa kan sauran abubuwan da suka zo a cikin yarjeniyar.
Jami’in na Hamas y ace a bangare na farko na Yarjeniyar HKI ta sabawa yarjeniyar a wuraren da dama, kamar bukatar a tsawaita bangare na daya ko kuma a sake sabuwar tattaunawa.
Hamdan ya yi allawadai da saba wa yarjejeniyar ta 1, wacce ta hada wurare 210, daga ciki har da hana wadanda aka kora daga gidajensu komawa inda suka fito, kashe Falasdinawa 116, jinkiri wajen sakin Falasdinawan da aka yi musayarsu. Da kuma hana shigar kayakin agaji cikin Gaza.
HKI dai ta hana shigar kayakin agaji wanda bangare ne na yarjeniyar, da kayakin sake gina asbitoci da sauransu.