Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar.
Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi suka halarci taron gaggawa na Doha, domin tattauna harin da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas a kasar Qatar.
Babban jami’in na Hamas ya yi kira ga shugabannin yankin da ke halartar taron da su mayar da Isra’ila saniyar ware a siyasance da ta fuskar tattalin arziki da kuma gurfanar da jami’an Isra’ila a kotunan duniya domin kawo karshen yakin kisan kare dangi a Gaza.
Naim ya kuma jaddada cewa, harin da Isra’ila ta kai kan tawagar Hamas a birnin Doha, ya zo ne a daidai lokacin da tawagar ke tantance wata sabuwar shawarar tsagaita bude wuta a Gaza.
“Mun nuna sassauci mafi girma na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza, amma sojojin mamaya ne, ta hanyar amfani da kisa da kuma sanya sharuddan nasu, ke kawo cikas ga duk wata yarjejeniya da za a iya cimma.”
Daga karshe ya bayyana cewa kungiyar Hamas tana sa ran taron zai dauki matsaya guda daya mai ma’ana tsakanin Larabawa da musulmi, da suka hada da tsagaita bude wuta nan take da kawo karshen yakin Gaza, da dage shingen da aka yi, da yanke duk wata alaka da Isra’ila, da gurfanar da isra’ila kan laifuffukan da ta aikata, da samar da falasdinu mai ‘yancin cin gashin kai, da Al-Quds a matsayin babban birninta, da kuma tabbatar da ‘yancin komawar ‘yan gudun hijira.