Hamas Ta Bukaci A Dauki Matakin Gaggawa Domin Kawo Karshen Kisan kiyashin Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu Hamas ta sake yin kira da a gaggauta daukar matakin kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu Hamas ta sake yin kira da a gaggauta daukar matakin kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce hare-haren da aka kai kan wasu gine-gine da kuma asibitin Kamal Adwan da ke birnin Beit Lahia da ke arewacin Gaza da kuma yunkurin tilastawa Falasdinawa yin hijira na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila na ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a Gaza.

Kungiyar ta kuma ce gwamnatin sahyoniyawan na ci gaba da aikata laifuka kan al’ummar Gaza duk da sammacin kama firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin soji Yoav Gallant da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yi.

Kungiyar Hamas ta yi kira ga kasashen Larabawa da musulmi da kuma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin da ke da alaka da ita da su dauki matakin kawo karshen yakin kisan kiyashi da ake yi a zirin Gaza tare da janye wa yankin Falasdinu kawanya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments