Abu Ubaida, mai Magana da yawun dakarun izzuddeen Kassam na kungiyar Hamsa, wadanda suke fafatawa da sojojin HKI a yankin kimani watanni 8 da suka gabata, ya bayyana cewa a dai dai lokacinda sojojin HKI suka aikata kissan kiya shi kan al-ummar Falasdinu a garin Nusairat a jiya Asabar, sannan suka kwato fursononisu 4 da ransu, a dai dai wannan lokacin ne kuma suka kashe wasu daga cikin Fursinonin.
Tashar talabijin ta Al-Ama ta nakalto Abu Ubaida yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa abinda sojojin HKI suka aikata a Nusairat kissan kare dangi ne wanda ya cancanci ya zama laifin yaki.
Ubu ubaida bai bayyana yawan Fursinmonin yahudawan wadanda sojojin HKI suka kashe a kokarinsu na kubutar da fursinoni 4 ba.
Abu Ubaida ya kara da cewa sojojin sun shiga tsakanin yan gudun hijira a nusairatn da fararen kaya, kamar suna daga cikin yangudun hijira, sannan bayan sun gani inda wasu Fursinonin suke suka aikata kisan kiyashin da suka aikata.
Majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza, ta bayyana cewa ya zuwa lokacin bada wannan labarin falasdinu 210 suka rasa rayukansu daga ciki har da mata da yara kanana, a yayinsa wasu kima 400 suka ji rauni.