Hamas: Bayanin taron kasashen Larabawa da na OIC na bukatar karin kokari don dakile ta’addancin Isra’ila

Kungiyar Hamas ta tabbatar da bukatar taron kolin kasashen OIC da kasashen Larabawa, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kan wajabta wa haramtacciyar kasar Isra’ila

Kungiyar Hamas ta tabbatar da bukatar taron kolin kasashen OIC da kasashen Larabawa, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kan wajabta wa haramtacciyar kasar Isra’ila dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan Gaza da Lebanon, tare da neman daukar matakin gaggawa na dakatar da ita daga shiga cikin tarukan Majalisar Dinkin Duniya, da kuma haramta sayar mata da makamai.

Kungiyar Hamas ta sanar da cewa, shawarar da taron kasashen Larabawa da na OIC suka yanke na bukatar karin kokari wajen ganin an dakatar da Isra’ila daga kai hare-hare, da kuma kai dauki ga al’ummar Palasdinu.

Har ila yau kungiyar ta jaddada cewa: Babban taron kasashen musulmi na kasashen Larabawa ya yi kira ga kwamitin sulhun da ya wajabta wa yahudawan sahyoniya su daina kai hare-hare kan Gaza da Lebanon.

Ta kara da cewa: “Mutanenmu suna jiran ‘yan uwansu Larabawa da Musulmai su yi amfani da damar da suke da ita a dukaknin bangarori don dakatar da ayyukan ta’addanci na Isra’ilai.”

A wannan  Litinin ne aka gudanar da babban taron kasashen Larabawa da na Musulunci a birnin Riyadh. Shugabanni da wakilan gwamnatoci bakinsu yazo daya a cikin jawabansu kan wajibcin dakatar da yakin da Isra’ila ke yi a Lebanon da zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments