Jaridar HKI ta “Haaretz” ta buga wani labari da yake cewa, sojojin HKI suna shirin kai wa Gaza gagarumin hari ta kasa bisa cikakken goyon bayan Donald Trump na Amurka.
Jaridar ta kuma ce; Harin na kasa da sojojin za su kai a cikin zirin Gaza,gagarumi ne a karkashin sabon babban hafsan hafsoshin soja Iyal Zamir.
Har ila yau, marubucin rahoton Amos Har’el ya kuma kara da cewa; A wannan karon sun yi imani da cewa gagarumin harin da za su kai wa Gaza zai sa su cimma manufofin da su ka sanya a gaba da aka kasa, a cikin tsawon shekara daya da rabi.
Daga cikin wadannan manufofin da ‘yan sahayoniyar suke son cimmawa da akwai rusa makamai da karfin kungiyar Hamas.
Jaridar ta kuma ce a daidai lokacin da ake maganar tattaunawa domin musayar fursunoni, HKI tana shirin sake amfani da karfin soja domin sake shimfida ikonta a cikin Gaza baki daya.
Danagne da rawar da Amurka take takawa a cikin abubuwan da suke faruwa, iyalan fursunoni wadanda suke da takardun zama, ‘yan Isra’ila a lokaci daya kuma Amurkawa, gwamnatin Amurka ba sanar da su cewa, Donald Trump yana cikin shirin bai wa Benjamine Netanyauhu cikakken goyon bayan idan ya zartar da fara kai hare-hare ta kasa akan Gaza. Haka nan kuma an sanar da cewa, ko kadan Trump ba zai yi wa Netanyahu matsin lamba akan dole sai ya koma kan batun musayar fursunoni ba ta ruwan sanyi.