Gwamnatin Tarayyar Nigeria Tana Shirin Sauya Dokar Yunkurin Kisan Kai

A karkashin wannan Shirin za a daina daukar wanda ya yi kokarin kashe kansa a matsayin mai laifi da ake daurewa a gidan kaso na
Hoton Ali Pate

A karkashin wannan Shirin za a daina daukar wanda ya yi kokarin kashe kansa a matsayin mai laifi da ake daurewa a gidan kaso na tsawon shekara daya.

Waccan dokar ta daure wanda ya yi kokarin kashe kansa amma bai mutu ba na tsawon shekara daya gidan kaso, ta samo asali ne tun lokacin mulkin mallaka.Haka nan alkami yana da zabin yankewa mai wannan laifin hukuncin dauri ko kuma biyan tara, ko kuma a hada masu duka biyun.

Ministan lafiya na yanzu, Ali Pate ya ce a karkashin dokar da ake aiki da ita, ana daukar wadanda suke kokarin kashe kawukansu a matsayin masu  laifi mamakon a kalle su a matsyin masu fama da  a lafiyar kwakwalwa da suke da bukatuwa a taimaka musu.

Haka nan kuma ya ce, gwamnati tana Shirin aikewa da majalisar dokoki sabon sauyin da za a yi a cikin tsarin dokar.

Pate ya kuma ce, batun kokarin kashe kai zai ci gaba da zama a matsayin Babbar damuwa a cikin tsarin kiwon lafiya, kuma daukar hakan a matsayin laifi, yana kashe gwiwar kokarin samun taimako na masu matsalar,kuma yana cin karo da siyasar kiwon lafiya ta kasa.

Ministan kiwon lafiyar na Nigeria ya bijiro da wasu alkaluma na hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) da suke nuni da cewa a kowace shekara da akwai mutane 300,000 da  suke kokarin kashe kansu. A tsakanin wannan adadin ana samun mutane 7,000 da suke daukar rayukan nasu. Ministan Ali Pate ya kuma kara da cewa; A karkashin sauyin da ake son yi wa dokar ana son rage yawan kashe kai da kaso 15 daga nan zuwa 2030.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted