Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Kafa Rundunar Daukin Gaggawa Don Magance Matsalolin Tsaro

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman a kasar don magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda kasar take fama das u. Jaridar Premium times ta

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman a kasar don magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda kasar take fama das u.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan tsaron kasar Muhammad Badaru yana fadar haka a lokacinda yake kaddar da wani bangaren na rundunar a barikin Kabala da ke barikin Jaje a kusa da birnin Kaduna daga arewacin kasar a jiya Litinin.

Badaru ya kara da cewa gwamnatin kasar tag a akwai butara da samar da irin wannan rundunar, saboda magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda aka dade ana fama das u, ko kuma wadanda suke tasowa nan da ca.

Ya kara da cewa rundunar da aka kaddamar a jiya litinin bangare ne na runduna mai sojoji 800 da za’a samar saboda wannan gagarumin aikin tabbatar da tsaro a kasar. Idan an kammala hurasda sojojin zasu zama abin dogaro a lokacinda ake bukatar daukin gaggawa a ko ina a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments