A yammacin ranar Alhamis da ta gabata ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka aukawa Falasdinawa masu ibada bayan sun gudanar da sallar tarawihi a masallacin Al-aqsa, inda suka kore su daga masallacin da karfi, tare da hana su yin I’itikafi a cikin masallacin.
Da yake tsokaci a cibiyar yada labaran Falasdinu, Ziad Abhais, mai bincike kan al’amuran birnin Kudus, ya jaddada cewa, matakin da gwamnatin sahyoniyawa ta dauka na hana masu ibadar I’itikafi a cikin masallacin Al-Aqsa wani mataki ne na cin zarafi da kuma muzgunawa hakkokinsu na addini.
Ya kara da cewa: Sojojin yahudawan sahyoniya suna amfani da hakan ne don shimfida ikonsu a kan masallacin Al-Aqsa, domin kuwa a shekara ta 2015 an ba da izinin yin I’itikafi a cikin wannan masallaci a duk ranakun watan Ramadan.
Hukumar bayar da agaji ta Musulunci a birnin Kudus ta sanar da cewa sama da masu ibada dubu 80 ne suka gudanar da sallar isha’i da tarawihi a harabar masallacin Al-Aqsa mai albarka a yammacin ranar Alhamis, wadanda akasarinsu mazauna birnin Kudus ne da yankunan da yahudawa suka mamaye a shekara ta 1948.
A daidai lokacin da watan Ramadan ya shiga, sojojin Isra’ila sun jibge dakaru masu yawa a birnin Kudus da kuma kewayen masallacin Al-Aqsa don hana Falasdinawa masu ibada shiga masallacin .