A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami.
Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran a tsagaita wutar yaki da gaggawa, da kai zuciya nesa.
Har ila yau, sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Nigeria wacce kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya rattabawa hannu a yau Asabar,14 ga watan Yuni 2025, ta jaddada cewa; yaki ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma hanyar diplomasiyya ce za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, girmama juna da aiki da dokokin kasa da kasa.,