Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Amince Iran ta Kai Hare-Hare Kan cibiyoyin Sojojinta Guda Biyar

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojojinta Wani jami’in sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojojinta

Wani jami’in sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci a ranar Talata cewa; Hare-haren da Iran ta kai a watan da ya gabata sun afkawa wuraren sojojin mamayar Isra’ila, matakin da tuni duniya ta amince da kai irin wadannan hare-hare kan cibiyoyin sojin mamaya.

Jami’in da ke magana da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ki bayar da karin bayani, ciki har da gano wuraren da abin ya shafa ko kuma irin barnar da harin ya yi ga kayayyakin aikin soja.

Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama  marasa matuka ciki kan haramtacciyar kasar Isra’ila a watan da ya gabata a matsayin mayar da martani ga hare-haren ba-zata da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a ranar 13 ga watan Yuni kan Iran  wanda harin ya auna fitattun shugabannin sojoji da masana kimiyyar makamashin nukiliyar Iran.

Harin na Iran ya sha mai da hankali kan birnin Tel Aviv da Haifa, matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida musamman wuraren da suke dauke da mutane masu yawa da kuma yankin kudancin Falasdinu da aka mamaye kusa da Beersheba, inda ake da cibiyoyin soji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted