Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza.
Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu.
Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane.
Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey ba kwararren dan jarida ba ne, mutum ne wanda ya shahara da watsa labarun karya ba tare da dogaro da wata hujja ba.
Bugu da kari bayanin ya sake jaddada matsayar Libya akan batun Falasdinu da kare hakkokinsu na su yi rayuwa a cikin mutunci a cikin kasarsu.
Tun a ranar 25 ga watan Janairu ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump yake magana akan fitar da Falasdinawa daga Gaza zuwa kasashen makwabta kamar Masar da Jordan,lamarin da kasashen biyu su ka yi watsi da shi.