Gwamnatin Kasar Rasha Ta Bayyana Mikawa Kasar Ukraine Dalar Amurka Biliyon 20 Da Amurka Ta Yi Fashi Da Makami Ne Kai Tsaye

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta yi allawadai da gwamnatin Amurka saboda mikawa kasar Ukraine, kudaden kasar Rasah da ta kwace har dalar Amurka biliyon

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta yi allawadai da gwamnatin Amurka saboda mikawa kasar Ukraine, kudaden kasar Rasah da ta kwace har dalar Amurka biliyon $20, kuma hakan yana matsayin fashi da makami.

Tashar talabijin ta Pressstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha tana fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa. Wannan sata ce kuma kasar Rasha tana da wasu shirye–shirye na kwace hakinta daga kadarorin kasashen G7 wadanda suka yi hakan.

A ranar talatan da ta gabace ce ma’aikatar kudi ko baitul malin Amurka ta bada sanarwan cewa ta fidda dalar Amurka biliyon 20 daga cikin kadarorin kasar Rasha da ake tsare da su, kuma an bada su ga kasar Ukraine, saboda taimaka mata ta murmure daga barnan da kasar Rasha take mata.

Gwamnatin shugaban Biden dai tana yin iya kokarinta na ganin ta kara tsananta takunkuman tattalin arziki a kan kasar Rasha kafin ta mika ragamar shugabancin kasar ga shugaba Trump a ranar 20 ga watan Jeneru na shekara mai zuwa.

Ma’aikatar kudin Amurka ta bayyana cewa ta mika wadannan kudade na Rasha ga Ukraine ne, bayan taron shuwagabnnin G7 na watan Octoban da ya gabata, inda suka bukaci a taimakawa kasar Ukraine da kudade wadanda kuma za’a fiddasu daga kadarorin Rasah da suka kwace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments