Ministan harkokin wajen kasar Jamus Annalena Baerbock ta bayyana damuwar kasar Jamus da yadda sojojin HKI suke kutsawa cikin yankunan yamma da kogin Jordan suna kissan Falasdiwa suna kuma rusa gidajensu da kuma lalata tituna, ruwan famfo, da wutan lantarki na mutanen yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baerbock tana fadar haka a yau jumma’a a lokacinda ta ke ziyarar aiki a birnin Amman na kasar Jordan.
Labarin ya kara da cewa kimani kwanaki 10 da suka gabata ne sojojin HKI tare da rakiyar manya manyan motocin buldoza suka kusta cikin garin Jenin da wasu garuruwa a arewacin yankin yamma da kogin Jordan suka kashe falasdinawa suna rusa gidajensu.
Banda haka sojojin yahudawan suna kokarin murkushe kungiyoyin Falasdinawa masu nuna Turjiya a yankin ne, musamman a garin Jenin.
Har’ila yau ministan ta bayyana cewa gwamnatin HKI a matsayinda na gwamnatin mamaye bisa dokokin kasa da kasa ya zama wajibi a kanta ta samar da tsaro a yankin yamma da kogin Jordan, wanda a bisa dokar Geneva bangare ne na kasar Falasdinu da aka mamaye.
Kasar Jamus dai na daga cikin kasashen Turai da suke tallafawa gwamnatin HKI da makamai a yakin da take fafatawa da Falasdinawa a Gaza, sannan tana murkushe jamusawa wadanda suke goyon bayan Falasdinawa a kasar Jamus.