Mataimakiyar sakatarin harkokin wajen kasar Amurka ce ta bayyana haka a jiya Jumma’a a dai-dai lokacinda tawagar kasar Amurka take son ganawa da shuwagabannin yan bindiga wadanda suka karbi iko a kasar Siriya bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad,
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a shekara ta 2017 ne gwamnatin Amurka ta sanya lada har dalar Amurka miliyon $10, ga duk wanda ya kamo mata Julani ta kuma mika mata shi saboda ayyukan ta’addanshi.
Barbara Leaf ta bayyana cewa sun gana da Ahmed Al-Sharaa, shugaban gwamnatin riko na kasar Siriya a jiya Jumma’a., inda yayi masu alkawalin aiki tare.
Gwamnatin Amurka dai ta rufe ofishin jakadancinta a kasar Siriya ne a shekara ta 2012 tare da sanya Jamhuriyya Check ta wakilceta a cikin al-amuranta a kasar ta Sirya, kafin haka dai gwamnatin kasar ta Amurka ta bayyana cewa, zata yi aiki da sabbin masu iko da kasar Siriya tare da wasu sharudda.