Gwamnatin Bahrain Ta Kara Kaimi Wajen Kama Yan Adawa Daga Ciki Har Da Yara Kanana

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana  tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna  kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma ya fito zanga-zanga a cikin kasar, daga ciki har da yara kanana. Musamman a tsakanin watannin Augusta zuwa watan Decemban shekara ta 2024.

Shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta ADHRB Hussain Abdullah yayi allawadai da kama yan adawa musamman yara kanana kimani 11 da mahukuntan kasar ta Bahrain suka tsare, ba tare da gabatar da su a gaban kotu ba. Har’ila yau tare da hana iyayensu ziyartarsu, ko kuma sanin inda suke.

Sannan akwai rahoton azabtar da wasu daga cikinsu, da hanasu abinci mai gina jiki da kuma rashin kula da lafiyarsu ko basu magani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments