Ma’aikatar tsaron ta Amurka ta sanar da cewa za ta baza zaratan sojojin kasar na “Marines” akan titunan birnin Los Angeles domin fuskantar tashe-tashen hankulan da ake yi domin hana korar ‘yan ci-rani ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar ma’aikata tsaron kasar ta ce; Tuni na shirya sojojin na “Marines” 700 domin su yi aikli da rundunar “National Guards” wacce tuni tana kan titunan birnin bisa umarnin shugaba Donald Trump domin kama ‘yan hijira ba bisa ka’ida ba.
Ministan tsaron kasar ta Amurka ya ce ; za a kai sojojin ne a cikin birnin saboda bayar da kariya ga muhimman gine-ginen gwamnatin tarayya da kuma dawo da doka da oda.
Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya fada a jiya cewa, ba manufarsa ganin yakin basasa ya barke a Amurka ba, amma kuma ya yi wa masu tayar da kayar baya a cikin birnin Los Angeles barazanar dandana kudarsu saboda yadda suke cutar da rundunar kasa ( National Guards.)
A gefe daya gwamnan Jahar ta California Gavin Christopher dan jam’iyyar Democrat ya yi suka da kakkausar murya akan Shirin aikewa da zaratan sojojin na Amurka akan titunan birnin Los Angelos, yana mai cewa bai kamata a kai sojoji a cikin titunan Amurka ba.
Gwamnan ya kara da cewa; Aikewa da sojoji zuwa titunan California, wani kokari ne na Trump domin kara raba kan al’ummar kasar.”