Guterres: Harin Isra’ila a kan a filin sauka da tashin jiragen sama na Sana’a yana da ban tsoro

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya  ya yi Allah wadai da yadda ake ci gaba da samun tashin hankali tsakanin dakarun Yaman da Isra’ila, yana mai

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya  ya yi Allah wadai da yadda ake ci gaba da samun tashin hankali tsakanin dakarun Yaman da Isra’ila, yana mai cewa harin da aka kai a filin jirgin saman Sanaa yana da ban tsoro.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun MDD ya fitar , Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi Allah wadai da ci gaba da tabarbarewar lamurra na tsaro a tsakanin Yaman da Isra’ila. Hare-haren da Isra’ila ta kai a filin tashi da saukar jiragen sama na Sana’a da tashar jiragen ruwa ta Red Sea da tashoshin samar da wutar lantarki a kasar Yemen na da matukar tayar da hankali.

Jiragen yakin Isra’ila sun yi luguden wuta kan tashar jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Sanaa da wasu wurare a kasar Yemen a jiya Alhamis, inda ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa mutane hudu sun rasa rayukansu sakamakon wannan harin ta’addanci.

Guterres ya nuna matukar damuwarsa kan barazanar kai harin bama-bamai kan wuraren ayyukan agaji a kasar Yemen, inda kashi 80% na al’ummar kasar suka dogara da taimako.

“Sakataren Janar na ci gaba da nuna damuwa matuka game da hadarin da ke tattare da kara ta’azzara yankin, ya kuma nanata kiransa ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su daina daukar duk wani matakin soji tare da yin taka tsantsan,” in ji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments