Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba.
Jaridar ta kara da cewa: Isra’ila ta ayyana wasu Karin makarantu wadanda Falasdinawa suke samun mafaka a cikinsu domin kai musu hare-hare a nan gaba. A lokacinda HKI ta kasa ganin mayakan Hamas a fili sojojinta sun koma kan kissan Falasdinawa fararen hula, wadanda suke samun mafaka a makarantu.
A cikin watanni da suka gabata sojojin mamayar sun kai hare-hare akan wasu gine-ginen 6 wadanda suka kasance makarantu ne, wadanda Falasdinawa maza da mata da yara suka maidasu wuraren fakewa daga hare-haren sojojin HKI, suka kai mutane 120 ga shahada.
A ranar Litinin da ta gabata ce, sojojin mamayar suka kai wani harin a kan makarantar “A’ishiyya” wacce ta zama sansanin ‘yan gudun hijira a garin Deir-Balah’ na tsakiyar Gaza. Suka kuma kai falasdinawa da dama ga shahada.
Amma suka bada sanarwan cewa, ‘yan ta’adda ne suke fakewa a cikin makarantar, ba tare da sun gabatar da wata shaida ta tabbatar da hakan ba.
A bisa wani rahoton na MDD ta fitar, ta ce kaso 95% na makarantun Gaza, sun lalace, a yayin da wasu kimani 400 su ka rushe gaba daya saboda hare-haren sojojin yahudawan. A ranar 26 ga watan Mayu da ya shude ne, sojojin HKI suka kai hare-harei a kan makarantar “Fahmi-Jarjawi” da take cike da ‘yan gudun hijira wanda shi ma ya yi sanadiyyar shahadar Faladinawa da dama.