Search
Close this search box.

Gobara Ta Tashi A Garin Safad  Na HKI Sanadiyyar Hare-Haren Kungiyar Hizbullah Daga Lebanon

Kungiyar ta Hizbullah tana cigaba da kai hare-haren mayar da martani akan HKI a cikin yankuna mabanbanta da suke karkashin mamaya. Mayakan Hizbullah Sun Kai

Kungiyar ta Hizbullah tana cigaba da kai hare-haren mayar da martani akan HKI a cikin yankuna mabanbanta da suke karkashin mamaya.

Mayakan Hizbullah Sun Kai Hari a kan  Barikin “Daud” na Haramtacciyar Kasar Isara’ila da can ne babbar shalkwatar sojan ‘yan mamayar a yankin Arewa.

A sanarwar da ta fitar bayan kai harin, kungiyar ta Hizbullah ta bayyana cewa; Saboda taimakawa al’ummarmu ta Falasdinu da suke jajurcewa a yankin Gaza, da kuma kare al’ummar Lebanon, kungiyar gwagwarmaya ta kai hare-hare a yau Laraba akan sansanin “Daud” ta hanyar harba gwamman makamai masu linzami.

Daga wannan sansanin ne dai sojojin HKI suke shiyar kai hare-hare a cikin Lebanon da kuma Syria.

Bugu da kari kungiyar ta Hizbullah ta kai wasu hare-haren akan matsugunin ‘yan share wuri zauna na :Hatsur” ta hanyar harba gwamman makamai masu minzami.

A garin Safad kuwa makamai masu linzamin da kungiyar ta HIzbullah ta harba sun yi sanadiyyar tashin gobara a sassa daban-daban.

Kungiyar ta Hizbullah ta harba makami mai linzami samfurin  “Ballistic” akan babbar shalkwatar kungiyar leken asiri ta Mosad daka Tel-Aviv”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments