Kungiyar fursunonin Falasdinu ta ce za a sako wasu karin Falasdinawa 110 daga gidajen yarin Isra’ila a yau Alhamis a mataki na uku na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas.
Ana sa ran galibin Falasdinawan da aka ‘yantar za su isa yankin Radana na Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye da misalin karfe 12:00 na safe agogon kasar, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu.
Wannan ba zai hada da fursunoni 20 da za a tura gudun hijira a wajen Falasdinu ba.
Kungiyar ta kuma fitar da jerin sunaye da shekarun fursunonin da za a saki wadanda suka hada da akalla yara 30.
Sakin da za’ayi wa Falasdinawan 110 a yau zai sanya adadin Falasdinawa da aka sako daga gidajen yarin Isra’ila zai kai 400 yayin da ake aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu duk da cewa Isra’ila na ci gaba da keta yarjejeniyar ta hanyar kai farmaki da samame.
Ko a baya baya bayan nan sojojin Isra’ilar sun kame wasu Falasdinawa da dama a yankin yammacin gabar kogin Jordan, ciki har da Falasdinawa 12 da aka kama a gabashin Kudus.