Gaza : UNICEF Ya Yi Tir Da Kisan Gillar Da Isra’ila Ta Yi Wa Yara Fiye Da 14,500

Asusun kula da kananen yara na MDD, (Unicef), ya tir da kisan gillar da Isra’ila ke wa yara a zirin Gaza. Ko a baya baya

Asusun kula da kananen yara na MDD, (Unicef), ya tir da kisan gillar da Isra’ila ke wa yara a zirin Gaza.

Ko a baya baya nan Isra’ila ta kashe mutane 50 a Gaza a rana guda.

Yara fiye da 14,500 ne Isra’ila ta kashe a kisan kiyashin da take aikatawa a Gaza inji Unicef.

Babbar darektar asusun na UNICEF, Catherine Russell, Ta yi kira da a dauki matakin gaggawa a duniya don dakile radadin da kananan yara ke fuskanta a kullum, wadanda ke ci gaba da fuskantar zubar da jini, yunwa, cututtuka, da sanyi a cikin kisan kare dangi.

Russell ta bayyana cewa duniya ta nuna halin ko-in-kula, yayin da a kullum yaran Gaza ke fama da tashin hankali.

Fiye da Falasdinawa 44,900 galibi mata da kananan yara ne suka rasa rayukansu sakamakon yakin da aka fara bayan da kungiyar Hamas ta kai harin ba za-ta a Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments