Tawagar HKI ta masu tattaunawa don tsagaita wuta a Gaza ta isa birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Alhamis.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran KAN na gwamnatin HKI tana fadar haka a shafinta na X (wanda ake kira Twitter a baya).
Labarin ya kara da cewa, ya zuwa yanzu dai babu wani labari dangane da yadda tattaunawar zata kasance, daga banganen Masar, Qatar da kuma kungiyar Hamasa ba.
Tattaunawa ta karshe wanda aka gudanar dai, an gudanar da ita ne a birnin Doha na kasar Qatar inda Amurka ta gabatar da yarjeniyar tsagaita wuta wacce shugaba Biden na Amurka ya bayar a cikin watan Yulin da ya gabata tare da wasu gware-gyare a cikinta.
Kungiyar Hamas dai ta rika ta yi watsi da yarjeniyar don ta, kawo wasu abubuwan da Hamas ba zata taba amincewa ba, daga cikinsu ta raba zirin gaza biyu, zuwa yankin Philidelphia dake gefen Gaza dake iyaka da kasar Masar, sannan arewacin gaza, inda sojojin HKI zasu ci gaba da rike shi ko an tsagaita wuta.
Hamas ta ce babu wani sojan HKI da zai rage a gaza matukar suna son tsagaita wuta. Dole ne sai ta fidda dukkan sojojinta daga Gaza kafin a yi maganar musayar Fursinoni.
Amma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu y adage kan cewa sojojin HKI sun koma Gaza ne har abada, ba randa zasu fita daga yankin.