Gaza: Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani  Zai Ci Gaba  Har Zuriya Mai Zuwa

MDD ta bayyana cewa a tsakanin kowadanne mutanen Gaza  4, daya daga cikinsu yana fama da yunwa. Mai Magana da yawun kungiyar Agaji ta tarayyar

MDD ta bayyana cewa a tsakanin kowadanne mutanen Gaza  4, daya daga cikinsu yana fama da yunwa.

Mai Magana da yawun kungiyar Agaji ta tarayyar turai, May Musa Sayegh, ta yi ta’aliki akan wannan adadin na masu fama da yunwa a Gaza, inda ta ce; Wannan shi ne hakikanin abinda yake faruwa a kasa, kuma ya shafi mata manya da ‘yan mata da kuma kananan yara masu yawa.”

May Musa Sayegh ta fada wa tashar talabijin din aljazira cewa; Wannan yanayin Sakamako ne na hare-haren tsawon shekaru biyu da kuma rashin samun damar shigar da kayan agaji,musamman a arewacin Gaza.

Sayegh ta kuma ce; ta fuskar kiwon lafiya, al’amurra suna kara tabarbarewa, domin mutane suna rayuwa cikin bakin talauci, ga shi kuma ba a kai musu kayan agaji mafi karanci na bukatun yau da kullum.

Haka nan kuma ta yi ishara da yadda cutuka suke yaduwa saboda karancin ruwa da kuma rashin magani, da hakan yake haddasa asarar rayukan mata masu ciki da kuma kananan yara.

Bugu da kari,Sayegh ta ce idan har ba a shigar da taimako cikin yankin da gaggawa ba, kuma ya zama da yawa wanda zai ishi mutane, to wannan matsalar za ta ci gaba da wanzuwa.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce a kowace rana HKI take karyawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted