Hukumomi a Gaza sun zargi sojojin Isra’ila da satar sassan jikin gawarwakin Falasdinawa tare da kira a binciki wannan “mummunan laifi.”
Darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza Ismail Thawabta, ya fada a ranar Jumma’a cewa sojojin “mamaya na Isra’ila sun mika musu gawarwaki 120 ta hannun kungiyar agaji ta Red Cross a cikin kwanaki ukun da suka gabata, amma mafi yawan sun zo cikin mummunan yanayi, suna nuna alamun kisa da kuma azabtarwa.
Thawabta ya ce akwai alamun shakewa da alamar igiya a wuyansu, lamarin da ke nuni da kisa da gangan.”
“Sassan gawarwakin mutane da yawa sun bace, ciki har da idanu, da sauran gabobin,” in ji Thawabta, wanda ya ce ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila “sun sace sassan jikin mutane yayin da suke rike da gawarwakin,” yana mai cewa hakan “laifi ne.”
Jami’in na Falasdinawa ya bukaci kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama da su gaggauta kafa wani kwamitin bincike na kasa da kasa don binciken lamarin.
A halin yanzu dai Isra’ila na rike da gawarwakin fursunonin Falasdinawa 735, ciki har da yara 67, in ji kungiyar fafutikar kwato gawarwakin Shahidan Gaza.