Gaza: Sojojin HKI Sun Rusa Masallatai Har Kimani 600 A Yankin Gaza Tun Ranar 7 Ga Watan  Octoban Da Ya Gabata

Ministan agaji da al-amuran addini a Gaza ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun lalata ko rusa masallatai 604 a gaza, wannan banda wasu kimani

Ministan agaji da al-amuran addini a Gaza ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun lalata ko rusa masallatai 604 a gaza, wannan banda wasu kimani 200 da suka lalata tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ya zuwa yanzu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, mafi yawanm masallatan suna kan bakin Tekun medeteranina da ke yammacin zirin na gaza ne.

Banda haka ya ce sojojin yahudawan sun lalata ko kuma tona gawakin falasdinawa a gidajen mutuwa kimani 60 a yankin sannan sun sace gawakin Falasdinawa kimani 1000 daga lokacin.

A wani bangare kuma, ministan ya ce sojojin yahudawan sun rusa gine ginen ma’aikatarsa har 15 sannan ma’aikatan ma’aikatar kimani 91 suka yi shahada ya zuwa yanzu. Banda haka sun rusa tashar radiyon Alkur’ani dake gaza, da reshen ma’aikatar dake Khan  Yunus da wasu wurare masu muhimmanci na ma’aikatar a zirin na gaza.

Ya zuwa yanzu sojojin yahudawa yan mamaya sun kasha Falasdinawa 35,386 mafi yawan mata da yara, sannan sun raba falasdinawa fiye da miliyon 1.5 daga gidajensu a zirin gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments