Search
Close this search box.

Gaza : Firaministan Senegal Ya Bukaci Kasashen Musulmi Da Su Kauracewa Isra’ila

Firaministan Senegal, ya yi kira ga kasashen musulmi da su kaurace wa gwamnatin Isra’ila tare da kara matsa kaimi na mayar da gwamnatin yahudawan sahyoniya

Firaministan Senegal, ya yi kira ga kasashen musulmi da su kaurace wa gwamnatin Isra’ila tare da kara matsa kaimi na mayar da gwamnatin yahudawan sahyoniya saniyar ware.

A yayin wani sabon gangamin goyon bayan Falasdinawa a birnin Dakar na kasar Senegal, ne firaministan kasar Ousmane Sonko ya bayyana hakan.

Wannan shi ne karo na farko tun soma yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, da wani babban jami’in kasar Senegal ya halarci zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Dakar babban birnin kasar Senegal.

“Kauracewa Isra’ila,” “Yancin Gaza,” “Netanyahu mai aikata muggan laifuka”,” na daga cikin taken da masu zanga-zangar suka rera a lokacin tattakin.

Da yake jawabi a wajen gangamin firaministan Senegal, ya yi kira da a kara ba da hadin kai a tsakanin kasashen musulmi don tallafawa Falasdinu.

 Ya kuma ce: “Dole ne mu yi kokarin ganin an samar da mafita ta siyasa wacce ita ce mafita ta mayar da kasar Isra’ila saniyar ware”.

“Dole ne a kakaba takunkumin tattalin arziki, siyasa da diflomasiyya kan Isra’ila, inji firaministan na Senegal Usman Sonko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments