Search
Close this search box.

Gaza: Dakarun Saraya Kudus Sun Wargaza Wata Tankar Yaki A Fafatawa Da Sojojin HKI A Gaza

Kamfanin dillancin labara IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayani wanda dakarun Saraya Kudsu suka fitar a safiyar yau Asabar kan cewa sun wargaza

Kamfanin dillancin labara IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayani wanda dakarun Saraya Kudsu suka fitar a safiyar yau Asabar kan cewa sun wargaza tankar yaki samfurin Mirkav ta HKI a gabacin garin Dirbalah dake tsakiyar zirin gaza.

Labarin ya kara da cewa dakarun sun yi amfani da bom samfurin Thaqib wajen wargaza tankar yakin.

Kafin haka dakarun sun bada sanarwa kakkabo wani jirgin sama wanda ake sarrafa shi daga nesa a garin Khan Yunus.

A wani labarin kuma sojojin HKI a birnin Kudud sun farwa masallata falasdinwa bayan sallar Isha a cikin masallacin Al-aksa, sannan a safiyar yau Asabar bayan sallar Asubaha sun tura wani jirgin sama wanda ake sarrafa su daga nesa wadanda suka cilla hayaki mai sa hawaye kan masallata falasdinawa a cikin masallacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments