Gaza: An Sake Zakulo Gawakin Falasdinawa 105 A Gaza

A cikin binciken da ma’aikatan agaji suka gudanar na kwanaki 17 a birnin Gaza sun zakulo gawakin wasu karin Falasdinawa 105. Tashar talabijan ta Presstv

A cikin binciken da ma’aikatan agaji suka gudanar na kwanaki 17 a birnin Gaza sun zakulo gawakin wasu karin Falasdinawa 105.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Laraba dangin shahidai 105 sun taro a unguwar Al-Taj na birnin Gaza don yin bankwana da shaidan bayan da aka jera sauran gawakin da aka gano na wadannan Falasdinwa a unguwa.

Jami’an agaji sun bayyana cewa an zakulo gawakin ne tare da taimakon wasu ma’aikata daga  kasar Masar.

A jana’izar dai Tagreed Al-Hanawi wanda diyarsa Dr Alia Ramzi Al-Hanawi da Mijinta da kuma yayansu 4 suka yi shahda ya halarci jana’izar, yana kuma cewa an shafe zuriyyarsu gaba daya. Amma a yau na godewa All..da na sami damar daukar gawakinsu da kuma yi masu sutura da binnesu cikin mutunci. Wannan ya dan rage mani zafin da nake ji.

Shugaban kungiyar Agajin ta zakulo wadannan gawaki Mahmoud Basal  Ya yi kira ga wadanda suke da sauran tausayi a duniya su yi kokari don ganin an kare ragowar falasdinawa fararen hula a Gaza.

Fawaz Ziyara daya daga cikin dangin wadanda suka yi shahada a ginin Al-Taj yace akalla mutane 300 suka rasa rayukansu a lokacinda wani babban makamin HKI ya fada kan ginin. Sannan har yanzun akwai wasu da dama a karkashin burbushin ginin.

Jami’an gwamnatin Gaza sun bayyana cewa akwai mutane akalla 8000 karkashin buraguzan gine-gine a Gaza wadanda ba’a ganosu ba.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted