Gaza : Adadin Wadanda Sukayi Shahada A Hare-haren Isra’ila Ya Kai 44,502

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta kiyasta adadin wadanda sukayi shahada a hare-haren Isra’ila zuwa 44,502 tun daga watan Oktoban bara. Hare-haren da jiragen yakin Isra’ila

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta kiyasta adadin wadanda sukayi shahada a hare-haren Isra’ila zuwa 44,502 tun daga watan Oktoban bara.

Hare-haren da jiragen yakin Isra’ila sun kuma, jikkata wasu mutum 105,454.

A cikin rahotonta na rana ta 424 na kisan kiyashin, ma’aikatar ta ce sojojin mamaya na Isra’ila sun yi kisan kiyashi guda biyu kan fararen hula a zirin Gaza cikin sa’o’i 24, inda suka kashe mutane 36 tare da jikkata wasu 96 da aka kai asibiti.

Falasdinawa da dama ne suka rasu da jikkatar wasu a safiyar ranar Talata sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a yankuna daban-daban na zirin Gaza.

Kusan kashi 70 cikin 100 na wadanda suka rasa rayukansu a yakin na Gaza, mata ne da kananan yara, in ji ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya.

Ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da yawan fararen hula da aka kashe a yakin Gaza, yana mai cewa bincike ya nuna cewa kusan kashi 70% na wadanda aka tabbatar cikin watanni shida mata ne da kananan yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments